Home / ENTERTAINMENT / Cutar shan inna: Gwamnatin jihar Kaduna zata yi wa yara miliyan 3 rigakafi cikin kwana 6

Cutar shan inna: Gwamnatin jihar Kaduna zata yi wa yara miliyan 3 rigakafi cikin kwana 6

Health worker tries to immunise a child during a vaccination campaign against polio at Hotoro-Kudu, Nassarawa district of Kano in northwest Nigeria, on April 22, 2017

A wani bayani da hukumar kiwon lafiya na kananan cibiyoyi ta fitar, huƙumar tace za’a gabatar da bada rigakafin tsakanin ranar 6 zuwa 11 ga watan Yuli 2017.

Huƙumar kiwon lafiya na kananan cibiyoyi na jihar Kaduna ta ce a shirye take don yi wa yara miliyan 3 masu shekaru 0 zuwa 5 rigakafi don kawar da cutar shan inna cikin kwana 6 daga ranar 6 ga watan Yuli.

Mataimakin mai ruwa da tsaki na fannin ilimin lafiya Hamza Ikara da jagoran ƙungiyar yan jarida kan kawar da cutar shan inna (JAP) Lawal Dagara suka gabatar da wannan bayani ranar talata 4 ga watan Yuli.

A cikin bayanin za’a gabatar da rigakafin daga ranar 6 zuwa ranar 11 na watan Yuli shekara 2017.

“Za’a gabatar da rigakafin a tituna, gidaje har ma da kasuwanni” inji huƙumar.

Ta kara da yiwa iyaye kira na su taimaka su gabatar da yaran su masu shekaru 0 zuwa 5 don yin rigakafin don kawar da cutar shan inna a jihar.

Bayani ya nuna cewa a shirye huƙumar take wajen kaddamar da yin rigakafin a ko wani lungu da ke fadin jihar cikin lumana.

A karshe huƙumar ta yaba ma sarakunan gargajiya, malamai, yan jarida da sauran al’ummar jihar don gudumawar  da suke badawa don kawar da cutar kuma tana fatan zasu cigaba da taimakon hukumar.

Source: Pulse Nig

About Prince Idowu Oyewumi

FULL NAME : PRINCE MUHAMMED S. OYEWUMI BIO.: Graphics Designer, I.T Expert & Photograaphy Expert Edu Qual. Bsc, Diploma, Nim Follow us Twitter: @mdee_coded Facebook: @https://www.facebook.com/pxclusive/ Instagram: @mdee_Cool Tel.: +2348085570405

Check Also

Sen. Dino Melaye dress up swagalicious (Nigerians Attacks)

”Are You A Bouncer Or Senator’ – Dino MelayeAsked As He Shares New Photo by …

Python Dance Is A Wonderful Exercise – Deputy Governor Of Abia State

Ude Chukwu, deputy governor of Abia state, says citizens of the state are comfortable with …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *